Posts

Showing posts from 2017

Tunatarwa

Image
A zamanin Sahabbai watarana anyi gobara awani Qauye daga cikin Qauyukan Madeenah. Daga jin labarin Gobarar sai duk Mutanen Qauyen suka tafi aguje domin su kashe wutar daga gidajensu. Duk sun tafi in banda wani mutum guda. Da aka tambayeshi mai tasa ba zai taho ba?,  sai yace ai shi wuta ba zata ta’ba cin gidansa ba. Da suka je suka samu nasarar kashe gobarar daga gidajensu sai suka ga lallai wutar nan bata ta’ba gidan wannan mutumin ba, amma ta cinye suk gidajen dake kusa da nasa. Don haka sukayi mamaki sosai. Da suka dawo suka tambayeshi menene sirrin abun? Kuma ta yaya ya tabbatar cewa Wuta ba zata ci gidansa ba?. Sai yace “Ai Manzon Allah (saww) ya sanar dani wata addu’a wacce idan ka fadeta Allah zai kiyayeka daga dukkan Musibu. Ga addu’ar nan kamar haka : “اللهم أنت ربي لا إله إلا أنت عليك توكلت وأنت رب العرش الكريم، ما شاء الله كان وما لم يشأ لم يكن ، لا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم. أعلم أن الله على كل شيء قدير Ùˆ أن الله قد أحاط بكل شيء علما، اللهم إني أعوذ بك

Yadda ake yin flashin Waya

Image
Da zaka tara masu amfani da waya, ka tambaye su mene ne filashing? Zasu gaya maka cewar filashing shine idan wayarka ta sami matsala a kai ta wajen gyara a gyarata. To haka abin yake a ilmance ko ba haka ba? Anan kasar tamu ta Najeriya idan kace ayi maka filashing ko kace wayar ka ta sami matsalar OS nata, kana ganin masana suna hada ta da wata ‘yar bakar waya, su kuma hada ta da Computer, sannan su kuma yi wasu ‘yan siddabaru, sannan su baka ita ka gani ta dawo dai dai kamar babu abinda ya taba samunta. To Me Ake Nufi Da Filashing Na Waya? Gaskiya mu a Najeriya da kuma sauran makwabtamu dake Afirka zaka samu bamu da tsari irin tsarin da sauran kasahen da suka cigaba su keyi, a kasa irin su America ko England irin su Saudi Arabia da dai makamantansu suna da wani tsari da, zaka sayi wayane da kuma layi a hade . Amma kuma filashing shine ka canza tsarin da waya ta zo da shi na amfani da  service zuwa amfani da wani wani service. ABIN DA SAUKI? Yi wa waya Flashing ba wa

Happy Sallah Ya jama'ar musulmi

Image
Asslamu Alaikum jama'ar musulmi inai mana barka da sallah da fatan kowa yayi sallah lafiya Allah ya karba mana iba dojin mu Ameen summa Ameen

Musha dariya

MUSHA DARIYA wani malamine ya tambayi yan class menene love ? sai wata yariya tace love is a chemical substance that react between two heart sai yace are you stupid sai tace stopid is a person who ask the meaning of love:

Best of photos

Mudassir  Abdurrahaman Gulu

Magana jari 2

Image
Da aku ya ga Sarki ya fusata sai ya ce, “Ka yi mini gafara bisa ga abin nan da zan fadi. Musa zai zama sanadin cuce-cuce, da raunuka, kai har da halakar rayukan mutane kamar dubu na kasan nan. Wannan al’amari kuwa ba da dadewa ba zai auki. Da ma kana ganewa, ka sake shiri tun da wuri.” Da Sarki ya ji haka sai ya hasala, don aku ya ce dansa zai za

Magana jari 1

Image
  A wani gari a kasashen gabas an yi wani babban Sarki wanda a ke kira Abdurrahman dan Alhaji. Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun Dankaruna, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda aka kawata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rike baki kawai, don abinya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa – kai! In ma mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarki Abdurrahman ga wadanda ba susan abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani shara ta yake yi. Amma duk yawan arzikin Sarkin nan sai ya zama na banza, don ba shi da ‘ya ‘ya, ba shi da kane, ba shi da wa. ‘Ya daya kadai gare shi, an ko yi mata aure, Saboda haka Sarkin nan ya zama ba wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da ‘yarsa kadai, abin da ya rage a sa baitulmali. Kuma sarautarsa sai wanda Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni’imomin duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa baki kirin. Ana nan ra

Magana jarice

Gabatarwa Wannan littafi, Magana Jari Ce, 1, yana cikin littattafai daga uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin zabo shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa ta rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko ‘Ruwan Bagaja’.   TSARIN LABARAN DAKE CIKI DAKI DAKI:   1. Magana Jari Ce 2. Labarin Wani Bororo Da Dan Zaki 3. Banza Ta Kori Wofi 4. Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku Taho Tare 5. Labarin Auta ‘Dan Sarkin Noma Da Naman Jeji 6. Labarin Sahoro Da Sahorama 7. Labarin Wani Bakauye Da Wadansu ‘Yan Birni 8. Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa 9. Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara 10. Labarin Kyanwa Da Bera 11. Labarin Wani Jaki Da Sa 12. Yadda Muka Yi Da Ubangijina Ojo 13. In Ajali Ya Yi Kira, Ko Babu Ciwo A Je 14. Labarin Wadansu Abokai Su Uku 15. Munafuncin Dodo, Yakan Ci Mai Shi 16. Abin Da Mutum Ya Shuka Shi Zai Girba, In Hairan Hairan

Musha dariya by Mudassir Abdurrahaman Gulu