Yadda ake yin flashin Waya
Da zaka tara masu amfani da waya, ka tambaye su mene ne filashing? Zasu gaya maka cewar filashing shine idan wayarka ta sami matsala a kai ta wajen gyara a gyarata. To haka abin yake a ilmance ko ba haka ba?
Anan kasar tamu ta Najeriya idan kace ayi maka filashing ko kace wayar ka ta sami matsalar OS nata, kana ganin masana suna hada ta da wata ‘yar bakar waya, su kuma hada ta da Computer, sannan su kuma yi wasu ‘yan siddabaru, sannan su baka ita ka gani ta dawo dai dai kamar babu abinda ya taba samunta.
To Me Ake Nufi Da Filashing Na Waya?
Gaskiya mu a Najeriya da kuma sauran makwabtamu dake Afirka zaka samu bamu da tsari irin tsarin da sauran kasahen da suka cigaba su keyi, a kasa irin su America ko England irin su Saudi Arabia da dai makamantansu suna da wani tsari da, zaka sayi wayane da kuma layi a hade . Amma kuma filashing shine ka canza tsarin da waya ta zo da shi na amfani da service zuwa amfani da wani wani service.
ABIN DA SAUKI?
Yi wa waya Flashing ba wai abi bane da kawai zaka shiga nan take domin ka karanta mukala kawai kace za kayi, Kana bukatar a kalla ace kasan computer a dan mataki na tsakiya, misali kamar kasan yadda ake daura program ko kuma kasan yadda ake cireshi, kuma a kalla kasan yadda ake shiga a gano wane driver ne babu a jikin computer kuma zaka iya yin wasu abubuwa fiye da haka.
Saboda yiwa waya filashing yana da nasaba da misalai dana kawo, domin dai dole farko kayi amfani da program na musamman da ake yiwa waya Flashing sannan kuma ace kana da wayar da ake kira da USB. Nasan mai karatu zai iya cewa wadannan abu guda biyar kacal mutum zai yi amfani da su wajen yin Flashing, wannan haka yake akwai program masu matukar yawa a internet wanda zaka iya saukar dasu a na’urarka kuma su taimaka maka wajen yin Flashing din wayarka.
Sabo da haka duk wanda yake da ilmin computer, kuma yana da program na Flashing sannan kuma yana da USB Cable lallai zai iya yin Flashing na waya. Da farko, sai ka fara saukar da shi program din idan baka da shi a computer ka, ko kuma kayi amfani da program na YOUR CELLULAR daga http://www.yourcellular.net/need help.htm Idan ka rubuta wannan adreshin internet zai kai ka zuwa ga shafin da zaka saukar da wannan program din da zai baka damar kayi Flashing na waya.
Da zarar File din ya sauko za a ganshi a zuge zai zo (zipped) sai a warware shi, idan kabi wannan tsari da zamu nuna maka tare da vedio da zamu saka nan gaba kdan zaka iya Flashing din waya cikin mintina ashirin (20).
Daga cikin abinda ya kamata da take tsaro CDMA wanda bayanin sa zai zo nan gaba.
ME ZAN BUKATA DOMIN INYI FLASHING DIN WAYATA?
1. Software na Flashing (wanda zaka sauko da shi daga internet).
2. USB cable wanda zaka hada wayarka da computer domin yin Flashing.
3. Computer wacce take da a kalla OS Windows 2000 zuwa sama sannan ta zamanto tare da USB port a jikinta sannan kuma ya zama tana da a kalla 256 RAM, da kuma saurin 800Mhtz.
4. Ya zama CDMA ce.
SHI NETWORK DIN ME YE AMFANIN SHI A FLASHING NA WAYA
Dangane da abubuwan da muka lissafa a baya na abubuwa guda hudu da ake bukatar ka mallaka kafin ka iya yin Flashing na waya sannan kuma dolene ya zamanto kana da account tare da daya daga cikin Alaro guda biyu wadanda a ke anfani da su a harkar sadarwar waya. Idan kuwa baka da su kana bukatar kayi rijista dasu don samun wannan dama. Wadannan manya manya alaro (carrier) da na fadi guda biyu cewar su suke bada network na waya, sune: Global System For Mobile Communication (GSM), sune kamar AT&T da T-mobile. Sannan Alaro na biyun shine CDMA ko kuma kace Code Division Multiple Access, misalinsu shine Quest da Metro da Sprint da kuma Verizon. wadannan sune tsari da ake da su na harkar sadarwa na Wayar-Tafi-Da-Gidanka, wanda wayar ka in ba GSM bace to dole ta zama CDMA wanda so da yawa ba mai iya banbancewa tsakanin su.
Sabo da haka wadannan sune hanyoyin fasaha da ake dasu guda biyar wadanda suke bayar da dama a samu network a wayoyin tafi da gidanka ko da yake a yanzu ana samun wayoyi masu karbar network biyu a lokaci guda.
Wannan shine a takaice abinda ake nufi da Flashing na Wayar-Tafi-Da-Gidanka a ilmance. ta daga wani tsari na kamfani. Misali ace ka sayi wayar MTN wadda dole sai da layin MTN ko kuma bata ma zo da shi ba kawai tana karbar service dinta kai tsaye daga MTN, sai aka wayi gari kana son ka yi amfani da wannan wayar amma kuma ba tare da ka canza waya ba, shine sai ka bi wannan tsarin, wanda idan kaje ka saukar da program da ake Flashing din waya ko dai GSM ce ko CDMA ce to zaka samu cewar idan ka sauko da file din akwai bayani dalla-dalla da zai nuna maka hanyar da zaka bi ka canza wayar ka ta koma tana amfani da ko wane layin waya, ko kuma ko wane irin service wanda a najeriyance ake kiran shi da cracking wanda a ilimi na computer a ke kiran shi da Flashing.
Zamu da kata a nan tukunna kafin fitowar mujallarmu ta gaba idan mai kowa da komai ya kai mu lokacin, zamuji yadda ake yin Flashing a Najeriya da kuma wasu ilmomi da suka shafi wayar tafi da gidan ka.
Comments