Magana jari 1

  A wani gari a kasashen gabas an yi wani babban Sarki wanda a ke kira Abdurrahman dan Alhaji. Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun Dankaruna, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda aka kawata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rike baki kawai, don abinya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa – kai! In ma mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarki Abdurrahman ga wadanda ba susan abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani shara ta yake yi.
Amma duk yawan arzikin Sarkin nan sai ya zama na banza, don ba shi da ‘ya ‘ya, ba shi da kane, ba shi da wa. ‘Ya daya kadai gare shi, an ko yi mata aure, Saboda haka Sarkin nan ya zama ba wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da ‘yarsa kadai, abin da ya rage a sa baitulmali. Kuma sarautarsa sai wanda Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni’imomin duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa baki kirin.
Ana nan ran nan sai ‘yan nan tasa ta haifi da namiji, aka yi shagali, aka sa wa yaron Malimudu. To, amma ko da ya ke Sarki ya yi murna kwarai da ya sami jika, duk da haka murnarsa ragaggiya ce domin dan mace ba ya gado, balle har a ce ya yi saraunta.
Yana nan cikin wannan bakin ciki, sai ran nan wani shaihun malami ya so ya ce masa, “Na yi mafarki jiya, a gaya mini da za ka tara malamai arba’in su yi ta yi maka addu’a har kwana arba’in, in Allah ya so za ka haihu.”
Sarki ya yi murna da wannan mafarki, ya dauko kudi da riguna zai ba malamin nan. Malamin ya ce shi ba kudi suka kawo shi ba, ya zo ne ya isad da umurni, ya yi sallama, ya tafi.
Ranar ba ta sake juyowa ba sai da Sarki ya sa aka tara masa manya malamai guda arba’in na kasarsa, ya gaya musu abin da ya ke so. Suka ce, “To, Allah ya karbi rokonmu!” Mutane suka ce amin. Suka yi shiri, suka shiga masallaci, suka duka.
Bangiji ya nufe su da katari, ya karbi rokonsu. Kwanan nan arba’in ba su cika ba sai da matar Sarki ta sami ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji, wanda kyaunsa ba shi da iyaka. Shagalin da aka yi cikin kasan nan, da farin cikin Sarki bisa ga wannan al’amari, ku da kanku kun san ba shi yiwuwa a bayyana shi cikin wannan dan karamin littafi. Aka dai fada wa yaron nan suna Musa. Watan tsakaninsu da jikan Sarki abin bai ko yi shekara ba.
Sarki kuwa ya dauki ransa ya kallafa bisa kan yaron nan. A ma tsaya a kwantanta son da Sarki ke wa dan nan nasa, abin ya zama kauyanci ke nan.
Kwanci tashi, bayan shekara biyu aka yaye yaron. Sarki kuma ya aika aka kawo jikan nan nasa Mahmudu, aka yaye su gaba daya, don su rika wasa tare. Suka tashi sai ka ce tagwaye, ba abin da ke raba su.
Da duk abin nan burin Waziri, tun da Sarkin nan ba shi ba da namiji, in ya mutu shi ya ci saraunta. Yana alla-alla Sarki ya mutu bai haihu ba, sai Allah ya kaddara haihuwar wanan yaro. Tun ran da Waziri ya ji gudar haihuwar Musa, zuciyarsa ta yi baki kirin, daga ran nan ya zama ko mai suna Musa ba ya so ya gani, ya shiga kulle-kulle kullum na yadda zai yi ya kashe Musa, ko kuwa ya sa ya bi uwa duniya, abin ya gagara. Har yara suka yi kamar shekara goma sha biyar biyar, ko ina Sarkin nan za shi da su ya ke zuwa.
Ana nan ran nan, ina ya Allah babu ya Allah sai Waziri ya sami wata dabara, ya ce a ransa ‘Alhamdu lillahi, ko-da-ya-ke ba yadda za a yi in sami Musa wani wuri shi kadai ba tare da Sarki ba, balle in san abin da zan yi masa, ai in na yi kokarin da na raba Musa da Mahmudu, kome ya yi kyau. Domin yadda suka shaku haka, lalle in aka raba su hankalin Musa zai tashi ta wannan hanya zan san yadda zan yi in sa shi ya sulale da dare ya bi dan’uwansa.” Sai ya yi dariya, ya buga kafa a kasa.
Kashegari, ko da ya tafi wagen fadanci aka fara ‘yan tade-taden duniya, sai ya takalo maganar yaki, ya ce, “Mu dai mun saki jiki da duniya yanzu, ba mu shirin kome.”
Sarki ya ce, “Me ya kawo wannanmagana, Waziri? Muna cikin sulhu haka, me ruwammu da wani shirin mayaka?”
Waziri ya ce, “Ai ka san ba a san abin da sauran kasashe ki ciki ba. Gwamma ko mu zauna da shiri, don ba a fafa gora ranar tafiya.”
Sariki ya ce, “Wane shiri ya wanda mu ke da shi yanzu? Ga Sarkin Yaki, ga Barde, ga Madawaki, cikinsu kowane ya yi kikan kura sai a ba shi hanya.”
Waziri ya ce, “Wadannan ai duk sun tsufa, ga Sairkin Yaki yanzu a kalla ya ba saba’in baya. Wanda ya ke haka, tun da Allah ya nufe shi da samun magaji, ya kamata ya huta. Dabarata sai Mahmudu ya koma gidansu, ubansa ya rika koya masa al’amuran yaki.”
Musa da ke nan sai ya tsolma baki ya ce, “In dai don a dauke Mahmudu ne, a bar ni ni kadai, ni ban yarda ba, sai dai mu je a koya mana tare.”
Waziri ya kau da kai ya kuta, ya ce, “Ina ruwanka da koyon yaki, kai da za ka sa a je a yi maka?”
Musa ya ce, “Ni dai ban yarda mu rabu ba.”
Sarki ya e, “Tun da musa bai yarda ba, dabararka ba ta yi ba ke nan, Waziri.”
Waziri ya bata fuska, zai fara wata magana sai ga wani ya zo ya fadi gaban Sarki, ya ce, “Ga Wazirin Sarkin Sinari ya zo da wadansu manyan garinsu, ya ce a yi masa iso.” Sarki ya ce ya shigo. Da ya shigo ya yi gaisuwa, ya mika masa takarda. Magatakarda ya karba ya buda, sai ya ga an rutuga:
“Takarda ta fito daga Sarkin Muminai, Sarkin Sinari, Abdul’azizi, dan Shahu Muhtar, zuwa ga masoyinsa amininsa Sarki Abdurrahman, gaisuwa mai yawa, da so, da yarda, da aminci. Amma bayan haka ina so in karfafa zumuntan nan da ke tsakanimmu, saboda haka na ba dana Musu ‘yarka Sinaratu, in sun kara girma a yi biki. Sai mu shirya a gama su tun muna da rai, Haza wasalamu.”
Da Sarki ya ji abin da takardan nan ke ciki sai ya tashi da fada, ya fizge takarda daga hannun, Magatakarda ya kyakke ta. Ya tashi ya kama gemun Wazirin Sinari, ya jefad da shi gefe guda. Sarakunansa suka shiga tsakani, suna “Hucewa mai duniya! Rashin hankali ne na yara.”
Sarki ya ce, “Ko Musa ya lalace ya auri Sinaratu? Me aka yi aka yi Sarkin Sinari, balle ‘yarsa Sinaratu?”
Ya dubi mutanensa, ya ce, “Ku yi ta dukansu sai sun bar kasata!”
Wazirin Sinari ya ruga, ya haye dokinsa, mutanensa suka dafi bayansa. ‘Yam birni suka bi su eho, eho. Fada duk ta rude, fadawa suka yi ta duban juna. Liman ya ce, “Allah ya ba ka nasara, abin nan da aka yi, a aika lafiya dai?”
Sarki ya ce, “me ya firgita ka? Don dai mai garin Sinari ko cewa na yi a mare shi, ya yi magana?”
Barde ya ce, “Ai Sarkin Sinari yanzu ganin kansa ya ke daidai da kowa. Ban yi tsammanin abin nan da aka yi masa zai kyale ba.”
Sarki ya ce, “Kai ma ka karai ne, kamar Liman?”
Waziri ya ce, “Ba karaya ba ce, ai gaskiya ce abin da na ke fadi yanzu na kan ba mu da shirin kome.”
Mutane suka ce, ‘Gaskiyarka, Waziri, ga Sarkin Yaki yau kwanansa kamar ashirin ke nan sai a kwantar a tayar, ba shi ko da magaji.”
Sarki ya kara fusata, ya ce, ‘Ba shi da magaji? Watau kun shiga maganar tsohon banzan nan? In dai maganar Mahmudu ku ke wa mita, na dauki alkawari, ko bai iya kome ba, duk yakin da ya fara tashi nan gaba, shi zai zama jagaba.” Aka gama fadanci aka watse, suka tafi suna zunden Waziri.
Waziri ya koma gida da fushi, ya kama shawarwarin abin da zai yi wa Sarki ya huce haushinsa. Daren nan ya kasa barci, ya kulla wannan ya kwance, har asuba. Da gari ya waye sai ya rubuta takarda zuwa wajen Sarkin Sinari, ya ce, “Kada wani abu ya ba ka tsoro da Sarki Abdurrahman, shirim ne ba inuwa. Muddin ka dauki alkawarin za ka nada ni Sarkin garin nan, ni ko na san yadda zan yi in taimake ka ka ci kasar. Domin duk mutanen kasar sai abin da na ce musu. Da farko sai ku dauri niyya maza ku zo kafin su shirya. Ku biyo ta kadarkon Kimba, don ta wannan hanyar har ka shigo birni kowa bai sani ba. Ku taho tare da wannan yaro ya nuna muki hanya, domin ko ban da shi nan kasar ba wanda ya san wannan hanya.” Sai ya ba wani amintaccen bawansa, wai shi Barakai, ya gaya masa yadda zai yi, ya sallame shi.
Sarki Abdurrahman kuwa bai sake komawa ta kan Sarkin Sinari ba. Ana nan ran nan ya sa aka daura wa dawaki sirada, ya hau tare da yaran nan suka tafi shan iska, har suka kai wata fadama, suka sauka suna hutawa, sai ga wani Balarabe dauke da aku cikin keji. Ko da Musa ya daga ido ya gan shi sai ya ce, “Alo, alo, ga aku a saya mana!”
Nan da nan wani bawan Sarki da ska je da shi ya kira Balaraben nan, ya tambaye shi kudin akun. Balarabe ya ce, “In ba jaka guda ba, ba na sayad da shi.”
Da bawan nan ya ji haka sai ya ce, “A’a! Da Sarkin za ka yi ba’a? Kana tsammani sarki ya tambaye ka karin magana ce?”
Da bawan nan ya fusata Sarki haka, sai ya cika ya ce a kama Balaraben nan. Bayin da aka zo da su suka tasam masa kamar za su cinye shi danye, da shi da tsuntsunsa duka.
Da dai tsuntsun nan ya ga haka, sai ya kada fifike, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, kada ka yi hushi bisa ga gaskiyar ubangijna. Ni ma a jaka gudan nan da ya fadi a ganina ya karya mini daraja ne. Kamata ai bai kamata a sallama ni jaka guda kadai ba.”
Sai sarki ya ce wa bayi su tsaya. Ya dubi dan tsuntsu, ya ce, “Kai kuwa dan tsuntsun nan mene ne dalilinka na wannan cika baki haka?”
Sai aki ya dukad da kai, ya ce, “Akwai kuwa, Allah ya ja zamaninka, takamar da na ke yi ba don saboda kyaun jikina kadai na ke yi ba, ba ko don saboda dadin bakin nan da Allah ya ba ni ba, amma saboda baiwa wadda Ubangijimmu ya yi mini ta wajen iya duba. Har yanzu ta kai ni fagen ina iya ba da labarin abin da za a yi nan gaba, balle ma a tambaye ni wanda aka yi ya iyaka. In kuma labaruruka ka ke son ji, ko na aljannu, ko na barayi, ko na Sarakuna, in ka saye ni in ya so ma kada ka sake batad da kudinka a banza garin sayen Alfulaila, ko wadansu littattafai na Turawa wadanda ba su da wani labari daga na tafiye-tafiyen gan kasashe, sai fa na tarihe-tarihe da na lissafe-lissafe, da na kiwace-kiwacen lafiya, masu gundurad da mutane. In kuma karuwa ka ke nema wurin arziki, in ka saye ni bukata ta biya.”
Sarki ya ce, ‘Ta wajen suruntun naka na wofi?”
Aku ya ce, “Surutu ba abin rainawa ba ne. Magana ai jari ce.”
Da yaran nan suka ji ya iya ba da labarai, da ma abin da su ke so ke nan, sai suka yi ta tsalle-tsalle suna murna. Sarki ya rike baki yana mamakin wannan tsuntsu. Sarki ya ce wa aku, “Tsaya mene ne na wanan irin fafarniya? Yabon kai jahilci. In kana da hikima, gaya mini yau shekarun Musa nawa?’
Sauran mutanen da suka zo tare da Sarki suka fashe da dariya, suka ce wa Sarki, “Allah ya ba ka nasara, ka ko kashe mana bakinsa! Ya fadi mu ki kan ba karya ba.”
Aku ya dubi Musa, ya ce, “Yau shekarunsa goma sha hudu da wata biyar d kwana uku.”
Mutane suka ce, “A’a! Ai ko, allah ya ba ka nasara, gaskiyarsa!”
Sarki ya ce, “Kai ji ya yi wajen wadansu ana fadi. Labarin musa yanzu ina ne bai kai ba?” Ya sake ce wa aku, “To, mun ji ka rike wannan da ka ji mutane ke fadi, amma wace rana ce aka haife shi?”
Aku ya sake duban Musa, ya ce, “Ranar Jumma’a da la’asar.”
Sarki ya ce, “A’a! Ai ko gaskiyarsa.” Ya dubi aku, ya ce, “Da ya ke kana da hikima, sai ka gaya mini me zai fara aukuwa gare shi?”
Aku ya ce, “Ba za ka so ka ji wannan al’amari ba, don zai bata maka rai kwarai. Ya fi kyau a bar kaza cikin gashinta.” Sarki dai ya nace sai ya gaya masa, in ya ki kuwa yanzu ya sa a hura wuta a babbaka shi da rai.

Comments

Mudassir Abdurahaman Gulu

Magana jari 2

Magana jarice

Musha dariya