A wani gari a kasashen gabas an yi wani babban Sarki wanda a ke kira Abdurrahman dan Alhaji. Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun Dankaruna, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda aka kawata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rike baki kawai, don abinya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa – kai! In ma mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarki Abdurrahman ga wadanda ba susan abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani shara ta yake yi. Amma duk yawan arzikin Sarkin nan sai ya zama na banza, don ba shi da ‘ya ‘ya, ba shi da kane, ba shi da wa. ‘Ya daya kadai gare shi, an ko yi mata aure, Saboda haka Sarkin nan ya zama ba wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da ‘yarsa kadai, abin da ya rage a sa baitulmali. Kuma sarautarsa sai wanda Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni’imomin duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa baki kirin. Ana nan ra